Faransa

Jam’iyar adawar Faransa ta UMP ta dauki matakin dinke barakarta

Tsohon shugaban kasar Faransa dan kuma Jam'iyar, Nicolas Sarkozy
Tsohon shugaban kasar Faransa dan kuma Jam'iyar, Nicolas Sarkozy

Jama’iyyar adawa ta UMP a Faransa, ta dauki matakin dinke barakar da ta kunno kai tsakanin ‘Ya ‘yan ta, lamarin da ya kawo rarrabuwan kanun shugabannin jama’iyyar.

Talla

Yanzu shugabannin da ke adawa da juna sun yarda a sake sabon zaben shugabancin jama’iyyar, a watan satumban shekara mai zuwa, don warware matsalar.
 

Bayan shafe wata guda ana takun saka , Jean-Francois Cope, da ya lashe zaben shugabancin jama’iyyar, da aka yi a watan da ya wuce, ya amince a sake zaben bayan tattaunawa ta wayar tarho da abokin hamayyar shi, tsohon Firaminista, Francois Fillon.
 

A baya Cope ya ki amincewa da duk wani zaben da za a shirya kafin zaben kasar na shekarar 2014.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.