Isa ga babban shafi
Algeria-Faransa

Ziyarata Algeria ba ta neman gafara ba ce, inji Hollande

Shugaba Hollande tare da takwaransa Abdelaziz Bouteflika  a ziyarar da ya kai kasar Algeria
Shugaba Hollande tare da takwaransa Abdelaziz Bouteflika a ziyarar da ya kai kasar Algeria AFP PHOTO/BERTRAND LANGLOIS/POOL

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande yace ziyarar shi a Algeria ba ta neman gafarar laifukan da Faransa ta aikata ba ne a Algeria a zamanin mulkin mallaka kamar yadda wasu suka bukata. Amma Shugaban yace ziyarar ta bude sabuwar danganta tsakanin kasashen biyu.

Talla

“Ziyarata Algeria ba ta neman gafara ba ce illa na kawo ziyara ne domin yin abinda ya dace” inji Hollande yana shedawa manema labarai.

Sai dai Shugaban ya amsa laifukan kasar Faransa da ta aikata wa mutanen Algeria a zamanin mulkin mallaka.

Kafin dai ziyarar shugaban wasu ‘Jam’iyyun siyasa guda 10 hadi da jam'iyyar ‘Yan uwa Musulmi sun bukaci lalle sai Faransa ta nemi gafara tare da biyan diyyar laifukan da ta aikata shekaru 132 da suka gabata.

Hollande yace Ziyarar shi ta dole ce domin inganta hulda tsakanin kasashen Biyu ta fuskar tattalin arziki da tsaro.

Shugaba Hollande dai ya samu tarba ta musamman daga shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika bayan kwashe lokaci kasashen biyu na adawa da juna musamman a zamanin mulkin Nicolas Sarkozy.

Akwai dai Miliyoyan mutanen Algeria da ke zama a Faransa kuma wasu daruruwa daga cikinsu sun sauya sheka zuwa Faransawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.