Rasha

Tsananin sanyi ya kashe mutane 88 a Rasha

Tsananin yanayin sanyi a kasar Rasha
Tsananin yanayin sanyi a kasar Rasha REUTERS/Mikhail Voskresenskiy

Tsananin sanyin da ake yi a kasar Rasha, ya yi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane 88 a sassa daban daban na kasar. Yanayi a kewayen birnin Moscow ya sauka zuwa 30 kasa da ma’aunin Celsius, ko 22 kasa da ma’aunin Fahrenheit, a daren jiya lahadi.  

Talla

Mutane bakwai da suka hada da wani karamin yaro ne suka mutu, cikin sa’oi 24 da suka wuce.
Jami’an gwamnatin kasar, sun umarci yara ‘yan makaranta sun zauna a gida, don kaucewa fadawa cikin matsalar.
Wata majiya daga asibitocin kasar, tace baya ga 88 da suka mutu, akwai wasu kusan 550 da ke bukatar kulawa ta gaggawa a asibiti.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.