Sweden

‘Yan adawa a Sweden sun koka da yawan Bakin –haure a kasar

Tutar kasar Sweden
Tutar kasar Sweden www.google.fr

Jagoran ‘yan adawan Sweden Stefan Lofven ya bayyana damuwar shi kan yadda bakin haure, da suka cika kasar, inda yace suna karbe ayyukan da ya kamata ‘yan kasar su yi.

Talla

Lofven, ya caccaki yarjejeniyar da jama’iyyar jariri hujja ta kulla da Green party a shekarar da ta gabata, inda aka sassauta dokokin shige da ficen kasar, ga wadanda basu kasashen kungiyar taraiyyar turai ta EU.
 

Rashin aikin yi, da ya haure da kashi 8 cikin 100 a watan Nuwamba, lamarin da ba taba gani ba tun shekarar 2010, ya zamanto babban kalu-bale ga gwamnatin PM Fredrik Reinfeldt, na jama’iyyar ‘yan mazan jiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.