Spain-SIDA

An gano allurar riga kafin rage kaifin cutar Sida a Spain

Wasu kwararrun likitoci a asibitin koyarwa ta jami’ar Barcelona da ke kasar Spain, sun ce sun samu nasarar gano wata sabuwar allurar rigakahi, da ke rage karfin cutar HIV ko kuma SIDA a kan wadanda ke dauke da kwayoyin wannan cuta.

Talla

Shi dai wannan sabon magani an yi gwajinsa ne a kan wasu mutane 36 da ke dauke da kwayoyin cutar ta HIV ko kuma Sida, kuma sakamakon da aka samu a kan wadannan mutane shi ne mafi inganci a cewar likitocin.

Dakta Felipe Garcia daya daga cikin kwararrin likitoci a asibitin koyarwa ta jami’ar Barcelona, wadanda kuma su ne suka samar da wannan sabon rigakahi, ya ce an tsara maganin ne ta yadda zai iya ragargaza kwayoyin cutar nan take, fiye da yadda sauran magunguna da aka taba ganowa a can baya.

A cikin makwanni biyu da soma gwajin maganin a kan wasu mutane 22, an fahinci cewa, karfin cutar ya ragu sosai a kan 12 daga cikinsu, kuma yanayin juriya da kuma share tsawon shekara daya yana aiki a jikin mai dauke da kwayar cutar ta HIV ko kuma Sida, wani abu ne da ya kara bambanta shi da sauran magunguna.

Kwararru a asibitin koyarwa ta jami’ar Barcelona, sun bayyaana gano wannan sabon rigakahi ne, a matsayin wata babbar nasara da aka samu a fannin kiwon lafiya a farkon wannan shekara ta 2013, domin ko ba komai zai rage wa, masu fama da kwayar cutar yawan shan magunguna barkatai a cewarsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.