Isa ga babban shafi
Birtaniya-Argentina

Cameron ya yi watsi da bukatar Argentina game da Falklands

Firaministan Birtaniya, David Cameron
Firaministan Birtaniya, David Cameron REUTERS/Darren Staples
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris
1 min

Firaministan Britaniya, David Cameron, ya yi watsi da bukatar kasar Argentina, na mayar wa kasar Tsibirin Falklands, wanda ya haifar da kace nace tsakanin kasashen biyu. Cameron yace mutanen tsibiran 3,000 sun bukaci ci gaba da zama karkashin kasar Britaniya, saboda haka babu dalilin da zai sa ya koma karkashin Argentina.

Talla

Britaniya ta karbe tsibirin ne shekaru 180 da suka gabata, bayan sun gwabza yaki a tsakanin su, inda yanzu haka Argentina ke bukatar ganin an mayar mata da Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.