Girka

Samaras ya tabbatar da yunkurin da Girka ke yi na magance matsalolin kasar

Firaministan kasar Girka, Antonis Samaras
Firaministan kasar Girka, Antonis Samaras REUTERS/John Kolesidis

Firaministan kasar Girka, Antonis Samaras, tabbatarwa da Shugabar kasar Jamus Angela Merkel cewa mutanen kasar na kokarin ganin cewa sun tsallake matsalar basussuka da suka addabi kasar.

Talla

Samaras wanda ya halarci wani taron bunkasa kasuwanci a birnin Berlin dake Jamus, ya gayawa ‘Yan jarida cewa, kasar tag Girka na shirin aiwatar da wasu tsare-tsare, a dai dai lokacin da ‘Yan kasar ke fuskantar matsanancin hali.

“Ina so na bada tabbacin cewa, Girkawa na daukan duk matakan da suka dace na ganin cewa an maido da al’amura dai dai ta fuskar tattalin arziki.”
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.