Jamus-ECOWAS

Jamus za ta ba ECOWAS tallafin jiragen yaki a Mali

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a lokacin da take ganawa da Alassane Ouattara
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a lokacin da take ganawa da Alassane Ouattara REUTERS/Tobias Schwarz

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel, tace za ta bai wa kungiyar kasashen Afrika ta Yamma jiragen soji biyu, don amfani da su a Mali, inda take cewa barin ta’adanci a Afrika na iya shafar lafiyar Turai.

Talla

Yayin da ta ke ganawa da shugaban kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, kuma shugaban kasar Cote d’Ivoire, Alassane Ouattara, Merkel tace za ta ba da jiragen cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.