Birtaniya

Birtaniya za ta mayar da hankali game da ta’addanci a taron G8

Firaministan Birtaniya, David Cameron
Firaministan Birtaniya, David Cameron REUTERS

Firaministan Birtaniya, David Cameron, yace zai yi amfani da matsayin shugaban kungiyar kasashe takwas da suka fi karfin tattalin arziki, wajen mayar da hankali akan barazanar aiyyukan ta’adanci, musamman abinda ya faru a Algeria da Mali.

Talla

Yayin da yake jawabi ga Majalisar kasa, Cameron yace barazanar kungiyar Al Qaeda da wasu kungiyoyin Masu aikata Jihadi a Arewacin Afrika, na bukatar matakan gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI