Birtaniya-Libya

‘Yan sandan Birtaniya za su kai ziyara Libya domin binciken harin Lockerbie

Firaministan Libya Ali Zeidan yana ganawa da David Cameron a wata ziyara da ya kai kasar.
Firaministan Libya Ali Zeidan yana ganawa da David Cameron a wata ziyara da ya kai kasar. REUTERS/Stringer

‘Yan sandan kasar Birtaniya da ke bincike akan tashin Bam da ya yi sandiyar mutuwar mutane sama da 200 da ke cikin jirgi Lockerbie a kasar Scottland, za su ziyarci kasar Libya domin ci gaba da gudanar da bincike.

Talla

Firaministan Birtaniya David Cameron ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gudanar da takwarsansa Ali Zeidan a lokacin da ya kai wata ziyarar ba-zata a kasar Libya.

A 1988 ne wani bam ya tashi a cikin jirgin ya kuma hallaka dukkanin mutane da ke ciki. Kuma wannan ne karo na farko tun bayan mutuwan tsohon shugaban kasar Moamer Ghadafi da hukumomin kasar Libya za su bar masu bincike su ziyarci kasar.

Ana zargin Abdelbaset Ali al- Megrahi ne da kai harin, wanda ya rasu bayan kasar Scotland ta sake shi daga gidan yari a shekarar 2012 bayan ya yi fama da cutar kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.