Birtaniya

Firaministan Birtaniya Cameron ya fara ziyarar aiki a kasar India

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron Reuters / Plunkett

Firaministan Britaniya, David Cameron, ya fara ziyarar aiki a kasar India, kasa da mako guda bayan ziyarar da shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya kai kasar. Cameron wanda ke tafe da ‘yan kasuwa da dama, zai sanya hannu a yarjejeniyar da ta hada da makamashi, tsaro da kuma ilimi.

Talla

Wannan na zuwa ne bayan India ta soke kwangilar jiragen yaki da kasar Italiya, sakamakon kama shugaban kamfanin saboda zargin bada cin hanci Dala miliyan 50 kafin samun kwangilar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.