Faransa-Girka

Faransa da Girka sun amince da yarjejeniyar tsaro

Ministan tsaron Faransa  Jean-Yves Le Drian
Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian REUTERS/Philippe Wojazer

Kasashen Faransa da Girka, za su sanya hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwar tsaro. Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian, da ke Magana bayan tattaunawa da takwaran shi na Girka, yace yarjejeniyar za ta kunshi samar da kayan aiki ga sojan ruwan kasar Girka, da suka hada da jiragen ruwan yaki.

Talla

Ministan Ya ce za a kafa wani kwamitin hadin gwiwa tsakanin kashen Biyu, don shata matakan yarjejeniyar.

Faransa, ta yi godiya ga hukumomin birnin Athens, kan gudunmawar da suka bayar a yakin kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.