Faransa

Sabon haraji ga kamfanoni da ma'aikata a Faransa

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande REUTERS/Fred Dufour/Pool

Wannan sabuwar siyasa ta tattalin arziki da shugaban Hollande ya alkawanta aiwatarwa tun a lokacin yakin menan zabennsa na shekarar bara, tuni dai Kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da ita, lamarin da ya tilastawa bangaren zartsawa sake zaunawa domin yi mata garambawul.

Talla

A karkashin wannan sabon haraji da gwamnatin ta ‘yan gurguzu ke neman aiwatarwa, duk wanni kamfanin, ko wani mutum kai hatta ma ma’aikacin da ke samu kudaden shigar da yawansu ya haura Euro miliyan daya a shekara, to za a zabtare masa kimanin kashi 75 bisa a matsayin haraji.

To amma a daidai lokacin da kamfanoni da kuma wasu ma’aikata ke kokawa dangane da wannan sabon salon biyan haraji, shi kuwa ministan kudin kasar Pierre Moscovici cewa ya yi, ai duka duka mutanen da suka cika sharudda biyan wannan haraji yawansu bai wuce dubu 30 ba a Faransa.

Idan dai har aka aiwatar da wannan doka, to ko shakka babu gwamnati za ta samu akalla Euro milyan 500 a shekara, adadin ya yi kadan matuka idan aka tantalum shi da gibin Euro milyan dubu 98 da kasafin kudin kasar ya fuskanta a shekarar ta 2012 da ta gabata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI