Fransa

Hollande ya ce za a kafa sabuwar doka don hana sulalewar haraji

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande Reuters/France2

A jawabinsa da wata tashar talabijin ta watsa a tsakiyar ranar yau, Francois Hollande ya ce a cikin ‘yan makwanni masu zuwa ne gwamnatinsa za ta gabatarwa majalisar dokoki da daftarin dokar kara kaimi ga ministoci da kuma ‘yan majalisun dokoki domin tabbatar da cewa suna gabatar da cikakkun bayanai dangane da dukiyoyin da suka mallaka.

Talla

Shugaban na Faransa wanda dama ke fuskantar suka daga abokan hamayyarsa na siyasa sakamakon karyar da ministansa mai suna Jerome Cahuzac ya shirga ta boye asusun ajiyar kudadensa a waje domin kaucewa biyan haraji, Hollande ya ce shi kam ba ya da masaniya a game da wannan coge na ministan balantana a ce ya ba shi wata kariya.
Daya daga cikin dalilan da suka sa ake kallon wannan batu da matukar muhimmanci ba wai a Faransa kawai ba, shi ne kasantuwar ministan kasafin kudin wanda ya kamata ya hana sulalewar masu biyan haraji, to amma kuma aka wayi gari shi ne ke gujewa biyan harajin.
Bazuwar wannan labari dai ya zo ne a daidain lokacin da Francois Hollande dan gurguzu ke ci gaba da fuskantar matsin lamba daga al’ummar kasar sakamakon karuwar marasa aikin yi da kuma shirinsa na halasta auren jinsi wanda shi ma ke samun suka daga milyoyin mutanen kasar,

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI