Birtaniya-Afghanistan

Birtaniya ta fara nazarin neman sulhu da Kungiyar Taliban

Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron
Firaministan Kasar Birtaniya, David Cameron REUTERS/Chris Radburn/POOL

‘Yan Majalisun Britaniya sun bukaci kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Taliban da ke kasar Afghanistan don samun zaman lafiya a kasar, yayin da sojojin kasar ke shirin ficewa. Kwamitin tsaro na Majalisar Birtaniya, yace kin kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Taliban na iya haifar da yakin basasa a cikin kasar.

Talla

Sakataren tsaron Britaniya, Philip Hammond, yace a shirye Britaniya take ta taimaka don kulla yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.