Fransa

Masu adawa da halasta auren jinsi sun yi zanga-zanga a Paris

Zanga-zangar adawa da halasta auren jinsi a brinin Paris
Zanga-zangar adawa da halasta auren jinsi a brinin Paris RFI/Sarah Elzas

Dubban mutane ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Paris na kasar Faransa a yau lahadi, domin nuna rashi amincewarsu da sabuwar dokar da gwamnatin kasar ke neman kafawa mai halasta auren jinsi.

Talla

Rahotanni sun ce daga cikin wadanda suka halarci zanga-zangar ta birnin Paris har da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar da suka fito daga jam’iyyun adawa wato UMP da kuma Front National.
A cewar ‘yan sandar da suka tabbatar da doka da oda a lokacin da masu zanga-zangar ke wucewa, akalla mutane dubu 45 ne suka karba wannan kira. Har ila yau an samu halartar wasu shahararrun ‘yan siyasa masu ra’ayin mazan jiya kamar dan majalisa Gilbert Collard da kuma takwaransa Nicolas Bay wadanda suka bukaci jama’a da su ci gaba da yi wa gwamnatin Francois Hollande matsin lamba domin yin watsi da wannan daftarin doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI