Korea ta Arewa

Korea ta Arewa na zargin Ba Amurke da shirya kifar da gwamnatin kasar

Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un
Shugaban Korea ta Arewa, Kim Jong-un REUTERS/KCNA

A yau Asabar Koriya ta Arewa ta ce za ta gurfanar da wani mutum Ba Amurke, dan asalin Koriya, da ya shiga kasar don yawon bude ido a bara gaban kotu domin tuhumar sa da yunkurin kifar da gwamnatin kwaminisanci ta kasar.

Talla

Hukumomin birnin Pyangyong sun ce za su gurfanar da da Kenneth Bae, mai shekaru 44, saboda laifukan da ake zargin ya aikata a kasar, lamarin da zai kara zafafa rashin jituwa tsakanin kasar, da Amurka, da da ma ba su ga maciji.
Kenneth Bae, na cikin wata tawaggar masu yawon bude ne da suka je ziyarar kwanaki 5 a birnin Rajin, a watan Nuwambar bara, kuma tun a wancan lokacin yake hannun ‘yan sanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI