Turkiya

Kasar Turkiyya ta zargi kasashen yammaci da yin shiru kan rikicin Siriya

Ahmet Davutoglu Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya da Johne Kerry na Amurka.
Ahmet Davutoglu Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya da Johne Kerry na Amurka. REUTERS/Osman Orsal

Ministan harkokin waje na kasar Turkiyya Ahmed Davotoglu, ya soki shirun da kasashen duniya sukayi masu da cewa shine ya haddasa rasa rayukan da ake cigaba da samu a rikicin kasar Siriya.

Talla

Ministan ya fadi hakan ne a yayin wata ziyara da ya kai a birnin Berlin na kasar Jamus cewa yadda duniya ta zuba wa Siriya idanu ko kusa bai dace ba.

Harin baya-bayan nan dai ya nuna yanda al’amurra ke cigaba da rincabewa sakamakon yanda kasa-dakasa ke cigaba da yin shiru a al’amarin kasar ta Siriya, a yayin da kwamitin tsaro na Majalisar dunkin Duniya ke cigaba da yin shiru kan aikin day a rataya akan shi.

Yace bai kamata a dandanawa al’ummar kasar Siriya da Turkiyya wannan matsalar ba.

Harin da aka kai a kan iyakar kasar Turkiyya day a yi sanadin mutuwar akalla mutane 46 wasu 100 suka jikkata shine mafi tsanani day a faru a kasar ta Turkiyya.
Don haka yayi kira ga samar da matakin kare aukuwar irin hakan a gaba, tare daukar matakan kai karshen fadan na kasar Siriya, kamar yanda yake cewa kasar Turkiyya nada ‘yancin daukar matakan kare kanta ga ire-iren wadannan hare-haren.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.