Faransa

Ana ci gaba da farautar mutumin da ya kashe sojan Faransa

Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban Faransa François Hollande REUTERS/Benoit Tessier

Jami’an tsaro na ci gaba farautar wani mahari da ya soke sojin kasar Faransa da wuka a wani lungun hada hadar kasuwanci a kasar ta Farnsa.Wani jami’in ‘yan sandan, ya bayyana cewar jami’ai masu kula da ayukan ‘yan ta’adda nacan suna aiki babu kama hannun Yaro domin zakulo wanda yayi wannan aika-aikar.Sai dai shugaba Francios Hollande ya bayyana cewar, ya zuwa yanzu ba zasu alakanta harin da wanda aka kaiwa sojin kasar Burtaniya a cikin makon day a gabata ba.Sojan da aka kashe, dake dauke da Bindiga cikin kaki, na aikin Sintiri ne daga cikin Sojin da aka sa domin gano maboyar ‘yan ta’adda a kasar.Maharin da aka bayyana shi a matsayin dan shekara 23 ya bace ko-sama-ko-kasa.