Turkiya

'Yan sandan Turkiyya sun janye daga dandalin Taksim

Wasu masu zanga zanga a kasar Turkiyya
Wasu masu zanga zanga a kasar Turkiyya Reuters/Umit Bektas

A yau Asbar ‘yan sanda a kasar Turkiya, sun janye daga dandalin Taksim dake tsakkiyar birnin Istambul babban birnin kasar, inda dubban masu zanga zanga suka mamaye tun jiya juma’a, suna masu nuna kyamar gwamnatin kasar.a jiya juma’a dai ne yan sanda suka mamaye dandalin, dake tsakkiyar birnin na Istambul, inda suka hana shigar ga masu zanga zangar, bayan da suka tarwatsa wasu daga cikin dandalin.Wannan kuma ya biyo bayan umarnin da Prime Ministan kasar Racep Tayyip Erdugan ya bayar ne, na tarwatsa masu zanga zangar dake nuna kin jinin gwamnatinsa mai ra’ayin Islama.