Turkiyya

An ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Erdogon

Masu zanga-anga a kasar Turkiyya
Masu zanga-anga a kasar Turkiyya Reuters/Umit Bektas

A yau kuma a dandalin Taksim da ke tsakkiyar birnin Istambul na kasar Turkiya inda dubun dubatar masu zanga zangar kin jinin gwamnati wanda ya haifar wa gwamnatin kasar mai ra’ayin Islama cikas a cikin kwanaki uku da soma ta.

Talla

PM kasar Recep Teyyip Erdogan ne, a jiya asabar ya bayar da umarnin sake buda dandali bayan da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga zangar, wacce yanzu haka ta soma bazuwa a sauran biranen kasar.

A yau ma ‘yan sandan sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa mutanen tare da kama wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.