Turkiyya

Ana Ci gaba da Bore A Kasar Turkiyya

Firaministan kasar Turkiya, Tayyip Erdogan
Firaministan kasar Turkiya, Tayyip Erdogan rfi

A kasar Turkiyya masu zanga-zangan kin jinin Fira Minista Tayyip Erdogan na ci gaba da karawa da jami’an tsaron kasar , yau kwana na uku a jere.‘Yan sanda sunyi ta fesawa masu bore ruwan zafi da hayaki mai sa kwalla domin Koran wadanda suka fara takakkiya domin isa ofishin Fira Minista Recep Tayyip Erdogan a biranen Istambul da Ankara.Masu bore na kururuwa suna la’antar Fira Minista da Gwamnatin sa, inda suke bukatar ya ajiye aikin haka.A halin da ake ciki Jakadiyar waje na kungiyar Kasashen Turai Uwargida Cathrine Ashton ta soki yadda ‘yan sanda ke amfani da karfin daya wuce kima wajen tunkarar masu zanga-zangan.