Faransa

Faransa na da sauran aiki kafin ta farfado da tattalin arzikinta.

Shugaban Faransa, Francois Hollande.
Shugaban Faransa, Francois Hollande. RFI / Romu Meigneux

Tattalin arzikin Kasar Faransa, kasa ta biyu wajen arziki a cikin kasashe masu amfani da kudin Euro ya fuskanci matsalolin a farkon wannan shekarar, inda aka sami dimbin marasa ayyukan yi, da rashin ayyuka.

Talla

Shugaban Faransa Francois Hollande ya yi ikirarin yin dukkan abinda zai yi domin farfado da tatalin arzikin kasar da kawo karshen rashin ayyukan yin nan da karshen wannan shekaran.

Sai dai kamar yadda rahoton Asusun ba da lamuni na duniya ke nunawa game da lamarin, Faransa za ta fuskanci matsala.

Acewar Asusun yadda aka sami matsaloli a karshen shekarar da ta gabata da kuma farkon wannan shekarar abu ne mai wuya akai ga nasarar abinda aka sa gaba.

A cewar Edward Gadner wani babban jami’in Asusun bayar da lamunin da ke Faransa bisa hasashen su matsalar rashin ayyukan yin a nan, kuma zai karu domin babu yadda za a magance matsalar a karshen wannan shekaran.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI