Turkiyya

Gwamnatin Turkiyya ta Lallashi Masu Bore

'Yan sanda na fafatawa da masu bore a Istambul, Turkiyya.
'Yan sanda na fafatawa da masu bore a Istambul, Turkiyya. rfi

Gwamnatin kasar Turkiyya ta roki gafarar mutanen da suka sami raunuka, sakamakon amfani da karfi da ‘yan sandan kasar ke yi domin murkushe masu bore a kasar.Mukaddashin Fira Ministan kasar Bulent Arinc wanda yake tattaunawa da manema labarai yau gameda wannan zanga-zanga, ya nemi jama’a dasu kwantar da hankali domin ana duba bukatun su.Mukaddashin Fira Ministan na magana ne bayan ya gana da Shugaban kasar Abdullah Gul.Yace suna bukatan kungiyoyi da jamiyyun Siyasa da sauran mutan kasar dasu kaunaci kasar tasu ayi tattalin zaman lafiya.Yace alkaluman dake hannun Gwamnati mutane 64 fararen hula suka sami raunuka, yayin da ‘yan Sanda 244 suka sami raunuka.