Faransa

‘Yan tawayen kasar Siriya sun kara jajircewa. Faransa tace Assad yayi amfani da Guba a Qusayr

‘Yan tawayen Syria sun ce zasu ci gaba da gwabza yaki da shugaba Bashar Assad duk da dakarun shi sun karbe ikon Qusayr da ke karkashin ikonsu.Tuni dai gwamnatin Iran ta aiko wa gwamnatin Assad da sakon taya murnar samun nasara kan ‘yan tawayen bayan kwashe kwanaki ana gwabza yaki a yankin na Qasayr.  

Talla

A wani labarin kuma kasar Faransa ta bayyana cewar tana da cikakkiyar hujjar data nuna cewar anyi amfani da Makamin Guba a fadan da ake cigaba da gwabzawa a Siriya.
Shugaban kasar Faransa Francios Holland y ace dole ne Duniya ta dauki mataki ga gwamnatin kasar Siriya kan kwararan hujjojin da suke da sun a cewar gwamnatin kasar ta yi amfani da Guba ga ‘yan kasar ta.
Farancios Holland yace yanzu suna da kwakkawarar hujjar cewar anyi amfani da Gubar, kuma lallai ne kasa-da-kasa su dauki mataki akan Siriya

Holland dai na jawabi ne a birnin Paris na kasar Faransa kwana daya bayan da Faransan ta bayyana cewar tanada hujja kan cewar Sriya tayi amfani da Sinadarin Sarin.

Itama kasar Burtaniya ta bayyana cewar tana da hujjar cewar Siriyar tayi amfanim da Sarin din, amma dai ta bayyana cewar zata jira har sai Majalisar dunkin Duniya ta kammala tantancewa da wannan labarin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.