Faransa

Mutuwar wani matashi a Paris

rfi

A kasar Faransa  an kashe wani matashi a birnin Paris a wani rikici da ya barke tsakanin wasu ‘yayan wata sabuwar kungiya ta ‘Yan adawa da gwamnatin kasar  Faransa. Bangarorin siyasar kasar dai  sun yi Allah Waddai da lamarin inda da dama suka yi kira ga gwamnati Shugaba  Francois  Hollande  da ta dauki matakan dakile bulluwar kungiyoyin da ke neman zama ‘Yan ta’adda a kasar Faransa.Hukumomin kasar  sun dau  alkawali  gudanar da  bicinke  a kai.