Faransa

An sami raguwar masu zuba hannun jari a Faransa

Shugaban Faransa François Hollande
Shugaban Faransa François Hollande REUTERS/Charles Platiau

Sakamakon wani binciken da aka gudanar, yace an samu gurguncewar masu saka hannayen jari a kasar Faransa, fiye da kasashen Birtaniya da Jamus a shekarar 2012.Sakamakon binciken ya nuna cewa Faransa ta samu faduwar masu saka hannayen jari da kashi 13, inda ya koma 471 daga 540 a shekarar 2012. Binciken ya nuna cewa kasar Birtaniya ta samu ci gaban da kashi 3 cikin 100, yayin da ita ma Jamus ta samu ci gaba da kashi 4 da digo 5.Kasar Spain ce dai a matsayi na hudu da Karin samun masu saka hannu jari kamar yadda binciken ya nuna.Faransa dai ta fi samun ‘Yan kasuwa daga kasar Amurka, a yayin da kuma attajiran kasashen yankin Asiya suka fi mayar da hankali a kasashen Jamus da Ingila.Daga cikin abubuwan da ake ganin yasa masu saka hannun suka fara kauracewa Faransa akwai matsalar haraji da kuma kudaden ayyukan biyan leborori.Sai dai kuma binciken yace an fi gudanar da aikin gaskiya a Faransa da kayutata rayuwar ma’aikata.