EU

An fara gangamin adawa da matse bakin aljihu a Girka

Wasu ma'aikata suna zanga zanga a Girka
Wasu ma'aikata suna zanga zanga a Girka Reuters/Yorgos Karahalis

Rahotanni daga Athens na kasar Girka na cewa kungiyoyin ma’aikata da jama’a daga kasashen Turai na halartar wani taron yini biyu, domin tsara fasalin adawar su, da  matakan da gwamnatocin kasashen su ke dauka, na matse bakin aljihu.Kungiyoyi sama da 300 ke halartan taron, inda suke sukar tsarin da Hukumomin kasashen nasu suka bullo dasu domin tada komadar tattalin arziki da suke fama.Kungiyoyin Likitoci daga kasashen Beligium da Faransa sun shiga zanga-zangar da takwarorin su suka yi a Athen na kasar ta Girka, domin nuna rashin jin dadi saboda yanke albashin likitoci da ma’aikatan asibiti da aka yi.Tun lokacin da kashen na Turai suka fada matsalar ta tattalin aziki, ake ta kokarin nemo hanyoyin da za shawo kan matsalar, da suka hada da matse bakin aljihu, lamarin da ma'aikta ke ci gaba da adawa da shi.