Faransa

‘Yan sandan Faransa sun kama babban jami’in kamfanin Orange

Stéphane Richard, Babban Jami'in kamfanin sadarwa na Orange
Stéphane Richard, Babban Jami'in kamfanin sadarwa na Orange AFP PHOTO/ERIC PIERMONT

‘Yan Sanda a kasar Faransa, sun cafke Babban jami’in kamfanin sadarwar Orange, Stephan Richard, saboda zargin da ake masa na hannu wajen biyan Dan kasuwa, Bernard Tape kudaden da basu kamata ba.

Talla

An kama jami’in ne saboda zargin da ake masa na taka rawa wajen amfani da kudaden Gwamnati, dan biyan attajiri, Bernard Tapie euro miliyan 285 diyya kan rugujewar bankin Credit na Lyonnais.

Wannan badakala dai ta dabaibaye shugabar Hukumar Bada lamini ta Duniya, Christine Lagarde, wadda ke rike da mukamin ministan kudi lokacin da aka biya kudin, yayin da Richard ke matsayin Babban hafsa a ofishinta.

Tuni Richard ya musanta aikata wani laifi a sanarwar da kakakin sa ya bayar inda ake saran zai kwashe sa’oi 24 yana amsa tambayoyi a gaban jami’an tsaro.

Har yanzu babu wani bayani da ya fito daga Kamfani Orange game da wannan batu.

Amma Christine Lagarde tace a shirye take ta kare kanta kan zargin da ake mata a wannan badakala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.