Faransa

An soke tashin jirage da dama sakamakon yajin aiki a Faransa

Filin sauka da tashin jiragen sama na Charles De Gualle a Paris
Filin sauka da tashin jiragen sama na Charles De Gualle a Paris Flickr/Caribb

Yajin aikin da ma’aikatan filayen sauka da tashin jiragen sama ke yi a kasar Faransa, ya yi sanadiyyar soke tashin jirage akkala dubu daya da dari takwas wadanda ke gudanar da zirga-zirga a cikin kasar da kuma wadanda ke zuwa daga kasashen ketare.

Talla

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Faransa, ta bukaci kamfanonin jiragen sama da su rage yawan tashin jiragensu da akalla kashi hamsin cikin dari, saboda karancin ma’aikata da ake fama da shi a cikin filayen jiragen sama.
Kungiyar ma’aikata masu kula da tashin jirage kasar, ta shiga yajin aiki na tsawon kwanaki uku a yau, da gobe da kuma jibi alhamis, domin nuna rashin amincewarsu da wasu sabbin matakai kan sufurin jiragen sama da Kungiyar Tarayyar Turai ke neman tilasta wa kasashen yankin yin amfani da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.