France

Faransa Na Gwajin Wani Katon Jirgin Sama Kirar Airbus A350

Fira Ministan Faransa a Toulouse yana wajen kaddamar da jirgin
Fira Ministan Faransa a Toulouse yana wajen kaddamar da jirgin rfi

Wani sabon Jirgin Fasinja kirar Airbus A350 kirar Faransa ya fara tashi domin gwaji yau Juma’a daga filin Jiragen Sama na Toulouse a kasar Faransa.Ya tashi ne daga Toulouse zuwa filin jiragen sama na Blagnac.Jirgin na dauke da maaikata shida da matuka biyu da suka yi yawon awa hudu a sama.Ana sa ran jirgin ya fara jigilan fasinja a tsakiyar watan shekara mai zuwa.An zuba kudin da suka kai euro miliyan 11 wajen samar da wannan jirgin fasinja.