Faransa

Ana cin kasuwar bajekolin jiragen sama a Faransa

Kasuwar Bajekolin jiragen Sama a birnin Paris
Kasuwar Bajekolin jiragen Sama a birnin Paris REUTERS/Pascal Rossignol

An fara bikin bajekolin jiragen saman kasar Faransa karo na 50, da ake kira Paris Air Show a turance, wanda kamfanonin hada jiragen sama daga kowane sako na duniya ke halarta. Kerawa da hada jiragen sama, na daga cikin bangarorin da ke taka muhimmiyar rawa a fagen tattalin arzikin duniya a wannan zamani.

Talla

Bikin bajekolin da ake gudanar da shi a Le Bourget, shi ne karo na 50, kuma ya samu halartar kamfanonin hada jiragen sama na zamani da jiragen yaki daga kowanne sako na duniya.

Tun kaddamar da bikin a shekarar 1909, bikin bajekolin ya zama wani dandali ko fage da masu harkar sufurin jiragen sama ke haduwa, da masu hada jiragen, don musayar ra’ayi da kulla huldar kasuwanci da kuma hadin kai kan yadda za’a inganta jiragen da ake da su yanzu haka.

Bikin, ba wai an takaita shi ne kan jiragen sufuri ba ne, domin ana baje jiragen yaki na soji, abinda ke bai wa hukumomin sojin kasashen duniya halartar bikin don ganewa idonsu irin ci gaban da aka samu wajen kera sabbin jiragen yakin zamani.

A ranar farko da fara bajekolin, an samu kulla cinikin Dala Biliyan biyar, inda kamfanin jiragen saman Amurka na ILFC ya bayar da odar kera masa jiragen Airbus A320 guda 50.

Za’a dai kwashe mako guda ana gudanar da bikin bajekolin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI