EU-Amurka

Kasashen Turai da amurka zasu bunkasa huldar kasuwancinsu

Taron ganawa tsakanin   Hermann Van Rompuy da Barack Obama da Jose Manuel Barroso daDavid Cameron game da huldar kasuwanci
Taron ganawa tsakanin Hermann Van Rompuy da Barack Obama da Jose Manuel Barroso daDavid Cameron game da huldar kasuwanci

Kungiyar Kasashen Turai da Amurka sun kaddamar da wani sabon yunkurin tattaunawar bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen su, Yayin da suke shaidawa manema labarai aniyar su, Fira Ministan Britaniya, David Cameron, yace suna Magana ne akan cinikin da zai zarce duk wanda ake da shi a tarihin duniya. Shugaban Barack Obama yace za’a fara taron farko a watan gobe a birnin Washington.