EU

Kungiyar EU na taro kan harkokin banki da bada tallafi

Wasu takardun kudin EURO
Wasu takardun kudin EURO REUTERS/Thomas Peter

Yau ministocin kudade na kungiyar kasashen Turai suka fara gudanar da taron su a birnin Brussels na kasar Belgium, kan shirin sauyi dangane da harkokin bankuna da kuma bada tallafi.Taron na zuwa ne a dai dai lokacin da ake samun rarrabuwar kawuna tsakanin kasashen na Turai, dangane da sauyin da ake shirin kawowa na harkokin bankuna da kuma bada rance.Bayanai sun ce, taron zai fi mayar da hankali kan matakan da za’a dauka na aiwatar da yarjejeniyar kaucewa fadawa cikin matsalar basusuka da kuma rugujewar bankuna.A baya kungiyar kasahsen Turai tace, asusun ta na EURO Miliyon dubu 500 na iya magance duk wata barazana da ka iya kunno kai a Yankin, amma har yanzu ba’a cimma matsaya kan nawa ne ya dace a baiwa bankin, da ya fada cikin matsala, daga kudin da ake bayar wa, na EURO Miliyon dubu 50 zuwa Miliyon dubu 70.Majiyar kungiyar tace, ministocin kasashen na fatan cimma yarjejeniya, tsakanin yau da gobe, duk da matsalar siyasar dake neman raba kan kungiyar a halin yanzu.