France

Ambaliyar Ruwa ta yi Barna a Faransa

Garin Lourdes inda ambaliya ta yi barna
Garin Lourdes inda ambaliya ta yi barna rfi

Sakamakon ambaliyar ruwa, a wasu sassan kasar Faransa wadda tuni ta haddasa hasarar rayukan mutane akalla uku, Hukumomin kasar na shirin ayyana yankunan a matsayin masu hatsarin gaske. Yankin kudu maso yammacin kasar Faransa ne  lamarin yafi kamari, domin hatta wuraren Ibadan kiristoci 'yan katolika dake kai ziyara da aka zaci ambaliayr ruwa za ta hana sakat na tsawon watanni, yanzu ana ganin ruwan zai dan ja bada dadewa ba,Sai dai kuma wasu yankunan sun kasance cikin hatsari saboda yadda koguna ke tumbatsa, domin saida aka rika kwashe dubban masu ziyara yankunan zuwa wasu yankuna gudun kada ambaliyan ta yi masu barna.Wannan gari na Lourde ya kasance wuri ne da mutane akalla miliyan 6 ke ziyarta duk shekaram domin a watan gobe da watan jibi, duk rana zaa sami mutane akalla dubu 40 dake ziyara a wannan gari, da aka ce Maryama mahaifiyar Yesu ta bulla a shekarav ta 1858, da aka gano akwai wuraren tarihi 68A bara irin wannan ambaliyar ruwa tasa anyi hasarar dukiya data kai kudin Euro kusan miliyan daya da rabi