Faransa-Nijar

Iyalan Faransawan da aka sace sun yi kiran a sake su

‘Yan uwan Faransawan da aka sace a nijar sun gudanar da gangamin kiran a sake su a Nantes yammacin Faransa
‘Yan uwan Faransawan da aka sace a nijar sun gudanar da gangamin kiran a sake su a Nantes yammacin Faransa AFP PHOTO JEAN-SEBASTIEN EVRARD

Bayan sace su da kuma ci gaba da yin garkuwa da su yau fiye da kwanaki dubu daya, ‘yan uwan Faransawa Hudu da aka sace a ranar 16 ga watan satumbar 2010 a garin Arlit da ke arewacin Nijar, sun bukaci da a gudanar da zanga zangar nuna goyon bayan ga ‘yan uwansu a kasar Faransa.

Talla

Wannan dai na a matsayin sabon salo na neman ganin an sako mutanen, wadanda aka sace lokacin da suke yi wa kamfanin hako Uranium na Areva da ke Arlit aiki, duk da cewa gwamnatin Faransa ta ce tana gudanar da aiki a asirce domin ‘yantar da wadannan mutane, Pierre Legrand, Daniel Larribe, Thierry Dol da kuma Marc Ferret.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI