Italiya

Kotun Italiya ta yanke wa Berlusconi hukuncin daurin shekaru 7

Tsohon Firaministan Itáliya Silvio Berlusconi
Tsohon Firaministan Itáliya Silvio Berlusconi REUTERS/Alessandro Bianchi

Kotun Italiya ta yanke wa tsohon Firaministan kasar, Silvio Berlusconi hukuncin daurin shekaru Bakwai a gidan yari tare da haramta masa rike wani mukamin gwamnati bayan kama shi da laifin yin amfani da kudi don ya yi lalata da wata karamar yarinya.

Talla

Alkalin da ya yanke hukuncin  ya zarce bukatun masu gabatar da kara wadanda suka bukaci a yanke wa Berlascuni hukuncin daurin shekaru Shida a gidan yari.

lauyan da ke kare Berlusconi yace alkalan da suka yanke hukuncin sun wuce gona da iri.

Akwai dai gungun masu zanga-zanga da suka bazama suna murna a harabar kotun bayan yanke hukuncin.

An kwashe tsawon shekaru biyu ana tabka shari’ar Berlusconi, amma ana iya wanke shi idan an kammala sauren daukaka karar shi a lokacin da ya ke zaman kaso.

Tsohon Firaministan na iya samun sassauci saboda shekarunsa karkashin dokar Italiya da ke wa masu shekaru sama da 70 lamuni a gidan yari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.