Faransa

An tsare Attajirin Faransa Bernard Tapie

Bernard Tapie yana gyaran riga  wanda  ke fuskantar tuhuma a Faransa
Bernard Tapie yana gyaran riga wanda ke fuskantar tuhuma a Faransa REUTERS/Charles Platiau/File

Masu Gabatar da kara a kasar Faransa, sun bayar da izinin tsare attajiri Bernard Tapie, saboda hannun da ya ke da shi wajen cin hanci da rashawar da ake wa shugabar hukumar bada lamuni ta Duniya, Christine Largarde.

Talla

Masu gabatar da karar na tuhumar shi ne da laifin karbar kudi euro miliyan 400 daga tsohuwar ministan kudin kasar, Christine Lagarde, daga asusun Gwamnati a shekarar 2008.

Tuni aka tuhumi uku daga cikin masu hannu a badakalar, cikin su har da shugaban kamfanin sadarawar Orange, mallakar Gwamnati Stephane Richard.

Rahotanni sun ce, Lagarde da yanzu ke shugabancin Asusun bada lamuni na Duniya, ta kauce ka’ida wajen biyan attaijirin, da zummar cewar zai taimaka wa shugaba Nicolas Sarkozy, a zaben shekarar 2007.

Tapie ya cika bakin cewar, babu abinda zai faru a hirar sa da tashar radiyon kungiyar kasashen Turai, saboda yadda aka tuhume shi sau bakwai, ba tare da samun sa da laifi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.