Faransa

An cafke karin mutane 3 da ake zargi da ta'addanci a Faransa

'Yan sandan Faransa gaban fadar Champs Elysées da ke Paris
'Yan sandan Faransa gaban fadar Champs Elysées da ke Paris AFP PHOTO BERTRAND LANGLOIS

Hukumomin tsaro a kasar Faransa sun cafke wasu mutane uku da ake zargin cewa ‘yan ta’adda ne a wani yanki da ke kudancin kasar.

Talla

Wannan lamari dai ya faru ne kwana daya bayan da aka cakfe wasu mutane uku a birnin Paris wadanda ake zargin cewa ‘yan ta’adda ne.

Ministan cikin gidan kasar ta Faransa, Manuel Valls. Ya tabbatar da cafke wadannan mutane, kuma ana tsare da su a yankin Canne-Ecluse da ke kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.