Italiya

Daure Berlusconi na iya rusa kawancen da ke karagar mulkin Italiya

Karima El Mahroug, da ake kira Ruby, da tsohon Firayi Ministan Italiya, Silvio Berlusconi
Karima El Mahroug, da ake kira Ruby, da tsohon Firayi Ministan Italiya, Silvio Berlusconi REUTERS/Stringer (L) and Sebastien Pirlet

Kwana daya bayan an yanke wa tsohon Fira ministan kasar Silvio Berlusconi hukuncin dauri a gidan yari, yanzu haka ra’ayoyi sun sha bambam a tsakanin al’ummar kasar Italiya dangane da makomar kawancen da ke kan karagar mulkin kasar.

Talla

Tuni dai wasu ‘yan siyasar kasar suka soma hasashen cewa akwai yiyuwar jam’iyyar Berlusconi, na iya ficewa daga cikin kawancen fira ministan kasar mai ci wato Enrico Letta, kuma yin hakan zai iya kasancewa sanadiyyar rushewar wannan kawance da aka kafa cikin watanni biyu da suka wuce.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI