Jamus-Turkiya-EU

Yunkurin Turkiya na shiga Kungiyar Turai ya gamu da cikas

Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Firaministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Osman Orsa

Kasar Jamus ta dakushe duk wani yunkurin ci gaba da tattaunawa tsakanin kungiyar kasashen Turai da Turkiya, a yunkurin kasar na samun wakilci a kungiyar, inda ta bukaci jingine tattaunawar na watanni hudu nan gaba, saboda yadda Turkiya ta murkushe masu zanga zanga. Ministan harkokin wajen Jamus, Guido Westerwelle, yace ba za su rufe idanunsu kamar babu abinda ya faru ba.

Talla

Kasashen Austria da Holland sun marawa Jamus baya wajen jinkirta taron.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI