Faransa

Kotun Faransa ta yanke hukuncin daurin ra-da-rai akan Carlos The Jackal

Ilich Ramirez Sanchez wanda aka yanke wa hukunci a Faransa
Ilich Ramirez Sanchez wanda aka yanke wa hukunci a Faransa REUTERS/Reuters Tv/Files

Kotun daukaka kara a kasar Fransa, ta daure Ilich Ramirez Sanchez, wanda ake wa lakabi da Carlos the Jackal rai da rai, saboda harin bama-baman da ya kai shekaru 30 da suka wuce.

Talla

Carlos mai shekaru 63 a duniya, dan asalin kasar Venezuela ne, ya kwashe sa’o’i 4 yana bayani wa kotun, amma alkalan ba su gamsu ba.

Ana dai daukar Carlos a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan ta’adda na duniya, wanda ya sha kai hare-hare kafin a cafke shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI