EU

Kungiyar EU za ta samar da aikin yi ga matasa a nahiyar Turai

Shugaban hukumar tarayyar Turai José Manuel Barroso
Shugaban hukumar tarayyar Turai José Manuel Barroso REUTERS/Yves Herman

Shugabannin kungiyar taraiyyar Turai ta EU, suna gudanar da taron su a birnin Brussels, inda suke fatan samar da aikin yi ga matasan kasashen yankin, da kuma kawo karshen shirin tsuke bakin aljihu, da ya janyo zaman kashe wando a tsakanin matasan. wani labari mai faranta rai, da ya fito daga zauren taron, ga matasan yankin ‘yan kasa da shekaru 25, su fiye da miliyon 5 da rabi da basu da aikin yi, shine kasafin kudin da aka amince da shi, na shekarar da zai samar da kudaden da za a yi amfani da su wajen samar musu aikin yi.An amince da yarjejeniyar ne, sa’oi kadan kafin fara taron na kwanaki 2.Bayan shafe watanni ana musayar yawu kan batun, shugaban hukumar ta taraiyar ta Turai Jose Manuel Barroso, yace shugabannin sun amince da kasafin.Ya ce kasafin kudin na EURO Miliyon dubu 960, zai taimaka wajen jawo hankulan masu zuba jari a nahiyar Turai, bayan ya sami amincewar ‘yan majalisar dokokin kungiyar ta EU su 754.Sai dai har yanzu kasashen da ke gaba gaba wajen aiwatar da shirin matse bakin aljihu, kamar su Britaniya, Jamus da Nethelands, da suka yi watsi da shirin karin kasafin kudi a farkon wannan shekarar, basu ce uffam ba kan wannan shirin.