Jamus

Jamus ta shawarci Masar da kada ta rusa turbar demokradiyarta

Ministan harkokin wajen kassar Jamus, Guido Westerwell a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida
Ministan harkokin wajen kassar Jamus, Guido Westerwell a lokacin da yake ganawa da 'yan jarida REUTERS/Osman Orsal

Kasar Jamus ta shawarci kasar Masar dake fama da rikici da kada ta rusa turbar demokradiyar kasar ta kuma nuna cewa tana cikin damuwa matuka game da rikicin da kasar ta shiga. 

Talla

Ministan harkokin wajen kasar Jamus, Guido Westerwelle ne ya bayyana hakan ya kuma kara da cewa kada ‘yan kasar su hasarar nasarar da suka samu na tunbike tsohuwar gwamnatin Hosni Mubarak.

“Muna kira ga daukacin ‘yan kasar Masar da su zabi hanyar tattaunawa a matsayin hanyar magance matsalar kasar.” Inji Westerwelle.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.