Belgium

Sarki Albart na Belgium zai mika mulki ga Dansa

Fadar Masarautar Belgium
Fadar Masarautar Belgium REUTERS/Francois Lenoir

Sarkin Belgium Albert na biyu ya tabbatar da Dansa a matsayin wanda zai gaje shi a gadon sarautar kasar bayan shafe tsawon shekaru sama da 20 a saman madafan iko. A ranar bukin 21 ga watan Juli ne Yarima Philippe zai karbi ragamar shugabanci daga Mahaifinsa. Firaministan kasar Elio Di Rupo ya bayyana fatar sabon Sarkin zai kasance cikin shiri domin daukar nauyin ayyukan da za’a daura masa.