Faransa

Hukumomin Faransa sun tabbatar da mutuwar Philippe Verdon

Shugaban Faransa, Francois Hollande
Shugaban Faransa, Francois Hollande REUTERS/Christian Hartmann

Faransa ta tababtar da cewar, gawar da aka samu na wani mutum a kasar Mali, lalle gawar Phillippe Verdon ce, wanda aka yi garkuwa da shi a watan Nuwamban shekarar 2011.

Talla

Shugaban kasar Fransa, Francois Hollande ya ce za’a mayar da gawar marigayin gida, kuma lalle Faransa za ta dauki fansa kan kungiyar Al Qaeda da ke Arewacin Afrika, wadda ta ce ita ta yi garkuwa da shi.

Verdon dai na daga cikin Faransawa 7 da ake garkuwa a wani wuri da ke cikin yankin Sahel, kuma AQMI ta ce ta sace su ne tare da yin garkuwa da su domin nuna bacin ranta dangane da irin rawar da Faransa ke takawa ta fannin yaki da ayyukan kungiyar musamman ma a Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.