Birtaniya

Majalisar Birtaniya ta amince da dokar auren jinsi guda

'Yan luwadi da masu goyon bayansu suna gudanar da zanga-zangar godewa 'Yan majalisar Birtaniya
'Yan luwadi da masu goyon bayansu suna gudanar da zanga-zangar godewa 'Yan majalisar Birtaniya REUTERS/Andrew Winning

‘Yan Majalisun Britaniya, sun kada kuri’ar amincewa da auran jinsi guda a England da Wales, matakin da ya bayar da damar fara daura auran daga shekara mai zuwa. Yanzu ana jiran Sarauniya Elizabeth ta biyu ta sanya hannu kan kudirin a cikin wannan makon don ganin ta zama dokar kasar.

Talla

Dubban masu kare hakkin ‘Yan luwadi ne suka gudanar da gangamin murna a harabar Majalisar bayan amincewa da kudirin.

Ana sa ran Sarauniya zata amince da dokar a ranar Laraba ko Alhamis.

Kasar Faransa ce kasa ta 14 da ta amince da auren jinsi guda a watan Mayu bayan kasashen Netherlands da Spain da Canada da Afrika ta Kudu da Norway da Sweden da Portugal da Iceland da Argentina da Denmark da Uruguay, da Belgium da New Zealand.

A kasar Amurka kuma akwai jahohi 13 da suka amince da dokar. Sai dai har yanzu akwai kungiyoyin musulmi da Kirista da ke ci gaba da adawa da dokar musamman a Faransa mai yawan Musulmi a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.