Italiya

Ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai zai yiwa kungiyar illa matuka- Italiya

Firaministan Italiya Enrico Lette
Firaministan Italiya Enrico Lette EUTERS/Giampiero Sposito

Firaministan Italiya, Enrico Letta, ya ce shirin Birtaniya na janyewa daga Kungiyar Kasashen Turai, zai yiwa kungiyar illa matuka.

Talla

Yayin da ya ke jawabi a London, bayan ganawa da takwaransa David Cameron, Letta ya bayan fatar sa na ganin mutanen Birtaniya su zabi cigaba da zama a cikin kungiyar.

Letta ya ce, ficewar Birtaniya daga kungiyar, ba zai haifar mata da mai ido ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.