Faransa/Myanmar

Hollande ya bukaci hukumomin Bama da su saki fursunonin siyasa

Shugaban kasar Faransa, Faransa Hollande (Hagu) da takwaransa na Bama Thein Sein (Dama)
Shugaban kasar Faransa, Faransa Hollande (Hagu) da takwaransa na Bama Thein Sein (Dama) REUTERS/Philippe Wojazer

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, ya bukaci takwaran aikinsa na kasar Bama wanda ke ziyara a birnin Paris, da ya gaggauta sakin fursunonin siyasa, sannan ya ci gaba da aiwatar da sauye-sauye a fagen tattalin arzikin kasar.

Talla

Hollande ya mika wannan bukata ne a lokacin da shugaban Bama Thein Sein ya kai ziyara a kasar ta Faransa.

Ziyarar wadda ita ce ta farko da wani shugaban kasar Barma ya ka kai a Faransa, ta zo a cikin wani yanayi na tashe tashen hankula masu nasaba da addini a kasar ta Barma, kuma kafin ganawarsa da shugaba Francois Hollande, shugaba Sein ya yi wata ganawar ta tsawon mintina 45 da Firaminista Jean-Marc Ayrault.

A wata sanarwa da fadar shugaban kasa ta Elysees ta fitar, ta bayyana cewa shugaba Hollande ya bukaci takwaransa na Barma da ya ci gaba da aiwatar da sauye sauye na siyasa da kuma tattalin arziki da ke kasar ta soma yau shekaru biyu kenan.

Sanarwar ta ce Francois Hollande ya bukaci takwaran aikinsa da ya saki dukkanin fursunonin siyasa da ke kasar sannan kuma a gudanar da bincike da hukuntar da masu hannu a rikicin addinin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a kasar cikin ‘yan watannin da suka gabata.

Kafin ya isa birnin Paris, shugaban na Barma ya kasance a birnin London na kasar Birtaniya inda ya sanar da cewa zai saki fursunonin siyasa.

A ranar 13 ga watan Yunin da ya wuce, kungiyar Tarayyar Turai ta bukaci hukumomin kasar da su kawo karshen kisan da ake yi wa Musulmi marasa rinjaye a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.