Birtaniya-Spain

Birtaniya na nazarin daukar matakin Shari’a akan Spain game da Gibraltar

Shingayen da Spain ta kafa a Yankin Gibraltar, da take takaddama da Birtaniya
Shingayen da Spain ta kafa a Yankin Gibraltar, da take takaddama da Birtaniya REUTERS/Jon Nazca

Birtaniya na tunanin daukar matakin shari’a kan yadda kasar Spain ta kakabawa mutanen Gibraltar shingayen ketare iyaka. Mai Magana da yawun fadar Firaminista David Cameron ya nuna bakin cikinsa da yadda Spain taki cire shingen a karshen mako.

Talla

Spain tace ta sanya shingen ne dan hana fasa kwabri akan iyakarta.

Rikicin kasashen biyu akan yankin na Gibraltar na ci gaba da kazancewa, inda Birtaniya ta yi gargadin daukar matakan shari’a yayin da kuma Spain tace za ta shigar da kokenta ga Majalisar Dinkin Duniya.

Yankin na Gibraltar yanki ne da bangarorin biyu ke ci gaba da tafiyar da harakokinsu domin bunkasa tattalin arzikinsu.

Amma gwamnatin Gibraltar tace Spain ta dauki matakan samar da shingen ne domin inganta kasuwancin kifi.

Birtaniya ta karbe ikon Yankin ne na Gibraltar a shekarar 1713 amma tun a lokacin ne Spain ke kokarin ganin yankin ya dawo mallakinta, lamarin da gwamnatin Birtaniya tace sai idan mutanen yankin sun amince.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.